IQNA

An Hallaka Babban Mufti Na ‘Yan ta’addan daesh A Mausil

23:52 - August 24, 2015
Lambar Labari: 3351071
Bangaren kasa da kasa, an hallaka babban mai bayar da fatawa ga ‘yan ta’addan Daesh a yankin Jazeera na kasar Iraki a wani harin jirgin yaki a rewacin birnin Mausil na gundumar Nainawa.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-alam cewa, a jiya an samu bababr nasara ta hallaka babban mai bayar da fatawa ga ‘yan ta’addan Daesh a yankin Jazeera na kasar Iraki a wani harin jirgin yaki a rewacin birnin Mausil na gundumar Nainawa a cikin Tal’afar na kasar.

Jami’an tsaron kasar sun ce samun samu babbar nasara ce bayan samun bayanan sirri dangane da wuraren da wadannan ‘yan ta’adda suke masu matukar hadari, kuma sun samu wannan nasara ne bayan kaddamar da hare-hare ta sama  arewacin yankin na tal’afar.

‘yan ta’addan daesh suna gudanar da wani zama a wani wuri na sirri wand aba su taba zaton wani ya sani ba, kuma an kai harin ne lokacin da suke wani zama a cikin wurin inda aka kashe su baki daya.

Rahoton ya kara da cewa, rundunar hadin gwiwa ta kasar Iraki tare da sauran rundunoni da jami’an tsaro a cikin lardin Nainawa, sn gudanar da wani aiki na bai daya a ranar Lahadi da ta gabata, inda suka kai farmaki a cikin wuraren buyar ‘yan ta’adda tare da ruda mafi yawan wuraren baki daya.

3350948

Abubuwan Da Ya Shafa: iraki
captcha