Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Press TV cewa, ya zuwa yanzu dai fiye da mutane 100,000 ne a kasar Birtaniya suka sa hannu, domin neman a kame Firayi ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu idan ya saka kafarsa a cikin kasarsu, domin gurfanar da shi a gaban kotun manyan laifuka ta duniya kan kisan dubban fararen hula da ya yi a yankunan Palastinawa.
Mutanen sun bukaci da a kame shugaban jam’iyyar ta Likud mai shekaru 65 da haihuwa a ziyarar da zai kai kasar a ranar Laraba mai zuwa, domin gurfanar da shi a kotun laifukan yaki kan farmakin da ya kai Gaza tsawon kwanaki 50 a jere yana lugudan wuta kan mata da kanan yara, kuma sa hannun ya kai na mutane 100,021 yau Asabar.
Wadanda suka sa hannun sun jadda cewa dole ne a kame Netanyahu saboda kashe fararen hul fiye da dubu 2 a cikin shekara ta 2014 da ya kaddamar da yaki kan fararen hula.
Bayan da sa hannun ya wuce 10,000 dole kan gwamnatin Birtaniya ta yi dubi kan lamarin, idan kuma ya kai 100,000 to dole e majalisar dokokin kasar ta zauna akan batun kuma ta sanar da matsayinta a kansa.
A hare-haren da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai Gaza a shekarar 2014 da ta gabata, ta kashe palastinawa 2200, kimanin 577 kuma kanan yara ne, yayin da wasu mutanen fiye da dubu 11 suka samu raunuka.
3358099