Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na oic-oci.org cewa, kungiyar za ta gudanar da zaman a matsayi na ministocin harkokin waje na kasanta domin tattauna batun ayyukan ta’addancin Isra’ila kan masallacin Quds mai alfarma, bayan da saudiyya ta bukaci agudanar da zaman.
Bayanin y ace wanann zama zai dubi ne kan irin abubuwan da yahudawan sahyniya suke yi kan wannan masallaci da sauran wurare masu tsarki na msuulmi da suke cikin birnin mai alfarma, da kuma sanin matakan da za a dauka kan hakan.
Iyad Amin Madani babban sakataren kungiyar ya bayyana cewa, bayan da kasar Saudiyya ta yi kira domin gudanar da wannan zama, tuni sun karba wannan kira, kuma za su gudanar da zaman a matsayi na ministocin harkokin waje na kasashen musulmi.
Tun bayan da yahudawan sahyuniya suka fara kaddamar da farmaki kan musulmi masallata a cikin masallacin aqsa amakon da ya gabata, gwamnatocin kasashen larabawa sun yi gum da baknansu, inda suka kasa yin koda alwadai ne da hakan.
Zaman zai zo daidai lokacin da za a fara babban taron zauren majalisar dinkin duniya, amma duk da haka ministocin harkokin wajen na kasashen msuulmi za su halarta omin sanin mataki na bai daya a cewar bayanin da ya kamata su dauka kan batun.
A cikin yan kwanakin nan dai haramtacciyar kasar Isra’ila tare da yahdawa masu tsatsauran ra’ayi sun zafafa kai farmaki kian masallacin quds mai alfarma, inda suke lakadawa musulmi masallata a cikinsa dukan kawo wuka.
3365174