Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na newnevvs.comcewa, dangin Sheikh Nimr sun tabbatar da cewa kotun daukaka kara ta masarautar saudiyya ta tabbatar da hukuncin kisa akansa.
Kungiyoyin kare hakkin bil adama da dama a kasashen duniya sun fara jan kunnen mahukuntan kasar Saudiyya dangane da hukuncin da wata kotun kasar ta yanke a kan daya daga cikin manyan malaman mazhabar shi'a a kasar, Sheikh Namir Muhammad Baqir Namir.
Kotun kasar ta Saudiyya dai ta yanke hukuncin kisa ne a jiya Laraba a kan Sheikh Namir, bisa tuhumarsa da sukar salon mulkin mulukiya na masarautar Al-saud a kasar ta Saudiyya a cikin hudubobin sallar Juma'a da yake gabatarwa a masallacinsa da ke yankin Awamiyya a cikin gundumar Qatif da ke gabacin kasar.
Gamayyar wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama a kasar birtaniya da ma wasu kasashen turai da na larabawa, sun gargadi mahukuntan kasar ta Saudiyya da su shiga taitayinsu a kan hankoronsu na ganin sun kashe Sheikh Namir, wanda a cewar kungiyoyin aiwatar da wannan hukunci na siyasa zai jefa kasar cikin wani mawuyacin hali, wanda masarautar kasar ce za ta dauki alhakin hakan.
Sheikh Namir dan shekaru hamsin da biyar da haihuwa ya sahara a kasar Saudiyya da ma kasashen larabawa, wajen gwagwarmayarsa ta kare hakkokin mutane da ake zalunta, da kuma bude cibiyoyin ilimi da wayar da kan al'umma kan harkoki na zamantakewa da kuma siyasa a addinance, wannan ya sanya shi ya samu karbuwa a wajen mutane da dama a kasar ta Saudiyya.
Mabiya mazhabar shi'a da ma wadanda ba su ba, musamman talakawa daga cikin mutanen kasar, sakamakon tunkarar sarakunan kasar da yake yi tare da fada musu gaskiya, abin da sauran malaman kasar ba za su iya yi ba.
A cikin watan Agustan 2008 gwamnatin Saudiyya ta kafa masa takunkumin na hana shi gabatar da laccoci ko fitar da makaloli da sauran rubuce-rubuce da ya saba yi, na addini ne ko na siyasa ko kuma na zamantakewa, tare da sanya idon jami'an tsaro a kansa.
Shugaban kwamitin tsaro da harkokin kasashen waje na majalisar shawarar Musulunci ya ja kunnen gwamnatin Saudiyya cewa zartar da hukuncin kisa a kan daya daga cikin manyan malaman Shi’a na kasar Sheikh Nimr Baqir al-Nimr za ta haifar da sabon rikici a yankunan da ‘yan Shi’a suka fi yawa a kasar.
Ya bayyana hakan ne a yau din inda ya ce zartar da hukuncin kisar da aka yanke wa Sheik al-Nimr zai haifar da gagarumin rikici a yankunan ‘yan Shi’an wanda ko shakka babu hakan ba zai yi kyau ga gwamnatin ta Saudiyya ba, don kuwa babu abin da Shehin malamin yayi face wa’azi da magana.
Wannan dai ba shi ne karon farko da jami’an jamhuriyar muslunci daban-daban suka ja kunnen Saudiyyan kan aiwatar da wannan hukuncin ba, don bayan da aka tabbatar da shi a jiya.
A jiya ne dai dan’uwan Shehin malamin ya bayyana cewar kotun koli ta kasar Saudiyyan ta tabbatar da hukuncin kisan da aka zartar a kan Sheik al-Nimr din a watannin baya saboda abin da suka kira tada hankali da kuma tunzura mutane su yi bore wa sarkin kasar.
3393817