Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Tena cewa, Darul Ifta babbar cibiyar bayar da fatawa ta kasar Masar ta fitar da bayani da ke kai hari kan masallatan musulmi a ko’ina haramun ne kuma aiki ne na ta’addanci.
Wannan bayani ya zo ne a matsayin mayar da martini ga kalaman wani muyum da ake kira Abu Lath da ke bayar da fatawa ga ‘yan ta’addan daesh da ke cewa za su ci gaba da kai hare-hare kan masallatan Shi’a kamar yadda suka yi a Najran na kasar Saudiyya.
Darul Ifta ta cewa masallatan shi’a da na ‘yan sunna duka bu daya wato dukkansu masallatai ne na muslmi da ake gudanar da bautar Allah madaukakin sarki, saboda haka babu wani dalili da ya halsta kai hari a kan masallaci.
Bayanin ya kara da cewa kai hari a kan masallaci tozarta wuri mai tsarki da ake bautar Allah, saboda haka yin wannan aiki ta’addanci ne kuma masu yin hakan sun shiga cikin babi masu barna a bayan kasa da suka cancanci fushin ubangiji, ba tare da cewa masallacin shi’a ko na snna ne ba.
Haka nan kuma bayanin ya kara da cewa, wadanda suke aikata wannan aki sun samu matsala ta fahimtar addini,a kan suke aikata ta’addanci da sunan addini, kamar yadda suke yi a halin yanzu a cikin kasashen Iraki da Syria, da kuma sauran kasashen musulmi da suke haifar da matsaloli na tsaro.
3426999