Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-hurrah cewa, David Lao babban malamin yahudawan sahyuniya a zantawarsa da tashar Al-hurrah ya bayyana cewa shigar yahudawa a cikin harabar masallacin Aqsa bisa ga abin da majalisar malaman yahudawa ta amince shi haram ne kuma yin hakan ya sabawa shari’ar addinin yahudanci.
David Lao ya ci gaba da cewa wasu daga cikin yan siyasar Isra’ila da kuma na Palastinawa suna kokarin baiwa wanann wuri mai tsarki wata sura ta daban wadda ba gaskiya ba.
Lao ya ci gaba da cewa ya zama a dauki dukkanin matakan da suka dace domin kawo karshen zam,an doya da manja da ake yi a tsakanin palastinawa da kuma yahudawa, domin hakan ba maslaha ce ga kowane daya bangaren ba, y ace dukakninsu suna girmama annabi Dawud (AS) da kuma Sulaiman (AS)
Ya jaddada cewa za su bi dukkanin hanyoyi na fadakarwa tare da jan hankali bisa koyarwar addininsu domin nuna wa mabiyansu wajabcin zaman lafiya atsakanin dukkanin al’ummomi na duniya da hakan ya hada da su kans yahudawa da kuma al’ummar palastinawa.
Dangane alaka da ke tsakanin bangarorin addinai kuwa, ya bayyana cewa addinin muslnci daya ne daga cikin addinai, kuma yana girmama akidun musulmi da suka yi Imani da su a matsayin addini gare su, domin kuwa babu inda aka ce a tsani wani saboda ko cin zarafinsa saboda addinansa da mahangarsa matukar dai ba ta sabawa yan adamktaka ba.
Ya ce duk wani abu na tashin hanakli da yada kiyayya baya daga cikin addinin yahudawa, balantana kisan kiyashi da kuma cin zarafin bil adama da yada kiyayya a tsakanin addinai da bil adama da wulakanta ko tozarta wurare masu tsarki na wasu addinai.
3439941