IQNA

Daesh Ta Rusa Wata Majami’a A Arewacin Mausil

22:29 - November 06, 2015
Lambar Labari: 3443994
Bangaren kasa da kasa, majiyoyin kungiyar mayakan kurdawa ta Peshmarga ta bayyana cewa yan ta’addan Daesh sun tarwatsa wata babbar majami’a a yankin Talkaif tazarar kilo mita 520 a rewacin Bagdad.


Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gioz na Al-alam cewa, a jiya yan ta’addan Daesh sun tarwatsa wata babbar majami’a bayan sun fitar da duk abin da ke cikinta sannan suka saka mata bam.



Wannan tarwatsewar bam ya jawo asarori masu yawa ga sauran gine-gine da suke yankina kusa wannan majami’a.



Shi dai wanann yankin dai yana karkashin kulawar dakarun na Peshmarga ne, kuma da dama daga cikin mazauna yankin na Talkaif mabiya addinin kirista ne.



Wadanda suke rayuwa tare da al’ummar wurin daruruwan shekaru lami lafiy ba tare da wata matsala ko tashin hankali ba kamar yadda yake faruwa  ahalin yanzu karkashin mulkin Daesh.



Yan ta’addan dai suna samun goyon baya ne daga wasu kasashen larabawa da suke makwaftaka da kasar, wadanda suke bas u tarin makamai da kudade domin rusa gwamnatocin da ba su shiri da su.



3443966

Abubuwan Da Ya Shafa: daesh
captcha