IQNA

Babbar Kungiyar Yahudawan Amurka Ta Yi Allawadai Da Isra’ila

23:52 - November 07, 2015
Lambar Labari: 3444464
Bangaren kasa da kasa, jagoran babbar kungiyar yahudawan kasar Amurka ya yi Allawadai da kakkausar murya dangane da zaluncin Isra’ila kan Palastinawa.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Press TV cewa, Reck Jekobez jagoran babbar kungiyar yahudawan kasar Amurka da ke neman zaman lafiya, a lokacin da yake jawabi a Ornaldo na jahar Florida ya yi Allawadai da kakkausar murya dangane da zaluncin Isra’ila  kan al’ummar Palastine marassa kariya.

Ya ce abin da haramtacciyar kasar Isra’ila take na mamaye yankunan palastinawa gabar yamma da kogin Jordan da sauran yankuna ya sabnawa kaida.

Jekobez ya kara da cewa wannan salon siyasar shi ne bababn abin da ya jawo rashin jituwa a tsakanin yahudawan Isra’ila da kuma palastinawa sakamakon zaluncin da yahdawan ke yi a kansu.

Y ace ba ma palastinawa ba kawai, hatta yahudawa wadanda suke na Orthodox ne suna fuskantar banbanci da wariya daga gwamnatin Isra’ila, kamar yadda kuma sauran yahudawa da suka zo daga Ethiopia suma suna fuskantar irin wannan matsala.

Rikici ya kara Kamari a birnin quds tun bayan da Isra’ila ta kafa dokar hana sauran palastinawa zuwa birnin daga sauran yankunansu domin gudanar da ayyukan ibada.

Ma’aikatar kiwon lafiya a palastinu ta bayar da rahoton da ke cewa, kimanin palastinwa 76 suka yi shada a cikin kwanakin na da suka hada da kanan yara 17, yayin da aka gina matsugunnai 120 tun bayan mamaye yankina  cikin shekara ta 1967.

3444235

Abubuwan Da Ya Shafa: amurka
captcha