IQNA

Mutane 3 Sun Rasa Rayukansu A Harin Kunar Bakin Wake A Kamaru

22:34 - November 10, 2015
Lambar Labari: 3446872
Bangaren kasa da kasa, mutane uku ne suka rasa rayukansu a wani harin kunar bakin wake da wasu mata biyu suka kai a kasar kamaru.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kasar Faransa cewa, akalla mutane uku ne suka rasa rayukansu a wani harin kunar bakin wake na bama-bamai da wasu mata suka kai a kusa da wani masallaci a cikin kasar kamaru a jiya.

Bayanin ya ce daya daga cikin matan ta tayar da bam da ke jikinta ta yi jigidarsa kuma ta tarwatsa kanta  akusa da masallacin, amma daya bata samu damar tarwatsa kanta ba, ganin haka sai jami’an tsaro suka harbe ta.

Babu wata kungiya ko wani mutum da ya dauki alhakin kaddamar da harin, amma dai kungiyar yan ta’adda ta Boko haram ita ce ta saba kai irin wadannan hare-hare a cikin kasar a cikin lokutan baya-bayan nan, bayan kai hari sau akalla 16 a cikin kasar.

Kungiyar ta yan ta’addan Boko haram tana mazauni ne a cikin tarayyar Nigeria, amma kuma tana fadada ayyukanta har zuwa cikin kasashe makawfta wato Kamaru, Chadi, da kuma Niger.

A cikin shekaru 6 da suka gabata hare-haren Boko Haram sun yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu 17, yayin da wasu kimanin 2.5 suka tsere daga yankunansu.

3446481

Abubuwan Da Ya Shafa: kamaru
captcha