IQNA

Wanda Ya Kashe Rai Kamar Ya Kashe Mutane Ne Baki Daya

16:38 - November 15, 2015
Lambar Labari: 3452917
Bangaren kasa da kasa, addinin muslunci bas hi da wata alaka da duk wani aiki na tashin hankali da dabbanci, a kan hakan e ya ce ; duk wanda ya kashe kamar ya kashe mutane ne baki daya, wanda kuma ya raya ta kamar ya raya mutane ne baki daya.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «FOX25» cewa, Sa’ad Muhammad daya daga cikin mambobin kwamitin da ke kula da harkokin musulmi a kasar Amurka ya nisanta ayyukan ta’addanci da addinin muslunci.

Ya ce abin da ake gani a halin yanzu daga yan tadda na kai hare-hare a birane na kasashen msuulmi da ma wadanda ban a musulmi duk da sunan addini, wannan babban kure ne, domin kuwa hakan yana nuna matsayin wadanda suke aikata hakan ne kawai.

Domin kuwa a cewarsa babu inda addinin mulsunci ya ce a kashe mutum babu gaira babu sabar, kuma idan mutan suka yi la’akari za su ga cewa abin da wadannan ‘yan ta’adda suke yi a kan musulmi ya muni a kan wanda suke yi a kan wadanda ba musulmi ba a cikin kasashe da dama.

Shi ma a nasa bangaren Iwad Nahad daya daga cikin mambobin kwamitin mai kula da harkokin mabiya addinin muslunci a kasar Amurka ya bayyana cewa ko shakka babu wadanda suke da aikata wannan lamari abin da suke yi ba shi da wata alaka da koyawar addinin muslunci da kurani mai tsarki.

Daga karshe ya yi kira ga mabiya addinin muslunci a kasar da su kara zama cikin fadaka domin kauce ma fadawa cikin irin wanann matsala ta rashin saitin tunani, kamar yadda kuma ya kira yi wadanda ba musulmi ba da su zama masu banbance Musulunci da abin da ba Musulunci ba.

3450651

Abubuwan Da Ya Shafa: amurka
captcha