IQNA

Sheikhul Azhar Ya Yi Allawadai da Harin Kasar Mali

22:56 - November 21, 2015
Lambar Labari: 3455352
Bangaren kasa da kasa, babban malamin Azahar ya yi Allawadai da harin ta’addancin da aka kai kan wani otel a Mali da cewa: muslunci ya barrabta daga hakan.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-wafd cewa, Ahmad Tayyib babban limamin cibiyar Azahar a kasar Masar ya bayyana cewa babu wata alaka a tsakanin addinin muslunci da kungiyoyin ‘yan ta’adda kamar yadda kuma babu alaka a tsakanin abin da suke yi da koyarwar Musulunci.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabia  gaban daruruwan malamai na cibiyar da kuma jami’ai na kasar, inda ya ce rashin aldalci ne a rika danganta addinin muslunci da kungiyoyi irin su daesh da makamantansu, domin kuwa ta’addanci ba ya da addini, Malamin ya yi Allawadai da kakkausar murya dangane da hare-haren da aka kai jiya a birnin Bamako na kasar Mali.

Daga karshe ya kirayi malamai da masana a kasashen musulmi da su mayar da hankali wajen wayar da kan al’ummomin duniya dangane da kuran da ake yi wajen danganta kungiyoyin ta’addanci da addinin Musulunci, tare da bayyana hakikanin koyarwar addinin muslunci wadda take koyar da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin bil adama baki daya.

Rahotonni sun bayyana cewa; Wasu gungun ‘yan bindiga a cikin wata mota mai dauke da lambar jakadanci sun shiga cikin harabar otel din da ke birnin Bamako fadar mulkin kasar Mali, inda suka fara gudanar da harbe-harbe suna kabbara, don haka jami’an tsaron Mali da suke yankin suka dauki matakin yin kawanya wa otel din tare da gudanar da musayar wuta da ‘yan bindigan, kuma jami’an tsaron na Mali sun yi nasarar ‘yantar da mutane da dama da suke cikin otel din.

3454947

Abubuwan Da Ya Shafa: azhar
captcha