IQNA

Mazauna Birnin Toronto Suna Bayar Da Kariya Ga Musulmi

20:56 - November 27, 2015
Lambar Labari: 3457472
Bangaren kasa da kasa, mazauna birnin Toronto suna gudanar da wani kamfe domin bayar da kariya ga musulmi a wuraren jama’a.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «Muslim Village» cewa mazauna birnin Toronto sun bullo da wata hanya ta bayar da kariya ga muuslmin birnin sakamamon halin da suke ciki.

Wannan kamfe dai an kirkiro shi sakamakon barazanar da mabiya addinin muslunci suke fuskamnta a halin yanzu sakamakon ayyukan ta’addancin da ake yi da sunan addinin muslunci.

Inda wasu daga cikin musulmi mazauan biranae na kasashen turai suke fuskantar wulakanci da cin zarafi da ke alfarma, tare da kiransu yan ta’adda, har da kai musu farmaki a wasu lokuta, wanda hakan yasa su cikin zullumi da dadarniya.

Wannan karan tsana da ake dorawa kan musulmi ya kara tsananta ne tun bayan kai harin da aka yi wanda yan ta’addan Daesh suka yi a birnin paris na kasar Faransa a makon da ya gabata.

Shi wannan shiri yana nufi kara kusanto da fahimta a tsakanin mutanen wannan birni, ta yadda za su gane cewa yan ta’adda daban musulmi kuma daban, kuma mabiya addinin muslunci ba su yarda da abin da wadannan yan ta’adda suke yi ba.

A wuraren hawan moton bus da kuma warren shiga jirgin kasa na karkashin duk an rubuta cewa ya kamata mu hada kai da musulmi mu zauna lafiya mu daina tsangwamarsu, da take kamar haka (#StandWithMuslimsTO)

A ranar Juma’a da ta gabata an gudanar da wata gagarumar zanga-zangar nuna goyon bayan ga musulmi a birnin Toronto wada shi ne mafi girma  akasar Canada.

3457397

Abubuwan Da Ya Shafa: canada
captcha