IQNA

Cire Daesh Na Daga Cikin Sabbin Ayyukan Telegraph

23:10 - November 28, 2015
Lambar Labari: 3457976
Bangaren kasa da kasa, masu kula da shafin sadarwa na zumunta na telegraph sun ce a halin yanzu za su iya gane mutanen da suke da alaka da kungiyar Daesh.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na an7a.com cewa, a cikin bayanin da suka fitar masu kula da shafin sadarwa na zumunta na telegraph sun ce daga  yanzu za su iya gane mutanen da suke da alaka da Daesh kamar yadda masu shiga shafin zasu iya gane hakan.

Bayanin ya ce idan aka duba Kalmar « report» za a iya shiga cikin bangaren da ake gane wadanda suke da alak da wasu ayyuka da ba su dace ba, kuma duk wanda ya ga hakan zai iya aikewa da nasa sakon domin duba abin abin wani yake ciki.

Ta wannan hanyar dann « report» za a iya shawo kan abubuwa da dama kama da batun yan ta’adda da kuma yada abubuwa masu alaka da lalata dabiun masu shiga cikin shafin.

Da dama daga cikin masu amfani da wannan manhaja ta sadarwa sun nuna gamsuwarsu matuka dangane da wannan mataki da kamfanin ya dauka, wanda kuma ake ganin zai amfanar da kowa, kama da su kansu kamafini har zuwa ga masu amfani da shi.

3457720

Abubuwan Da Ya Shafa: daesh
captcha