IQNA

Vilayati Ya Gana Da Sayyid Hassan Nasrullah

23:32 - December 01, 2015
Lambar Labari: 3459311
Bangaren kasa da kasa, babban mai baiwa jagoran juyin juya halin mulsunci shawara kan lamurra na kasa da kasa ya gana da babban sakataren kungiyar Hizbullah.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Press TV cewa, Ali Akbar Vilayati mai baiwa jagoran juyin juya halin mulsunci shawara kan lamurra na kasa da kasa ya gana da Sayyid Hassan Nasrullah babban sakataren kungiyar Hizbullah a birnin Berirut.

Ali Akbar Vilayati ya tattana batutuwa da dama da suka danganci halin da a ke ciki a yankin gabas ta tsakiya.

Muhimman lamurran da tatatunawar bangarorin biyu ta fi mayar da hankali a kansu shi ne halin da ake cikia  yanin, musamman ma batun yaki da ta’addanci wanda manyan kasashen duniya da karnukan farautarsu suka hadda sa a cikin wasu kasashen yankin, inda ya yi fatan kawancen da ke tsakanin Iran, Hizbullah, Syria, Rasha, Lebanon da kuma Iraki zai yi nasara.

Ya jaddada cewa ko shakka babu yan ta’adda da masu goyon bayansu ba za su nasara  akan al’ummar musulmi ba da ma na yanking abas ta tsakiya.

Sayyid Hassan Nasrullah a nasa bangaren ya bijiro da wasu daga cikin muhimamn lamurra da suka danganci yanayin da ake ciki na yaki da yan ta’adda a yanking abas ta tsakiya.

3459073

Abubuwan Da Ya Shafa: Hezbollah
captcha