IQNA

Ayatollah Sistani ya Gana Da Gwamnan Tehran

23:43 - December 03, 2015
Lambar Labari: 3459636
Bangaren kasa da kasa, Ayatollah Sayyid Ali Sistani babban malamin addini a kasar Iraki ya gana da gwamnan birnin Tehran a yau a ziyarar da ya kai Iraki.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Fars cewa, Muhammd Ghalibaf magajin garin birnin Tehran ya kai ziyarar aiki a Iraki inda ya gana da Ayatollah Sayyid Ali Sisran a gidansa.

Babban marja’in ‘yan Shi’a a kasar Iraki Ayatullah Sayyid Ali Sistani ya bayyana wajibcin kokari wajen kawo karshen makice-makircen da makiya suke kullawa al’ummar kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labaran Fars na Iran ya bayyana cewar Sayyid Sistani ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da magajin garin Tehran, babban birnin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a ziyarar da ya kai masa a gidansa da ke birnin Najaf na kasar Iraki, inda yayin da yake magana kan kokarin da makiya suke yi na cutar da ‘yan Shi’a ya bayyana cewar: Manufar makiya ta kirkiro kungiyoyi irin su Taliban, qaeda da daesh ita ce kawarwa ko kuma raunana kasashen musulmi irin su Siriya da Iraki, don haka sai Shehin malamin ya ce wajibi ne a yi dukkanin abin da za a iya wajen kawo karshen wannan makircin.

Ayatullah Sistani ya bayyana cewar matsalar kasar Siriya da Iraki, wata matsala ce ta duniyar musulmi da wajibi ne a bata muhimmanci.

Magajin garin na Tehran dai ya tafi kasar Irakin ne don halartar taron juyayin Arba’in na Imam Husain (a.s) da za a gudanar a kasar Irakin a gobe Alhamis, kamar yadda ofishin Sayyid Sistanin ya fitar.

3459427

Abubuwan Da Ya Shafa: iraki
captcha