IQNA

Idan Da Daesh Sun San Kur’ani Da Ba Su Kashe Mutane Ba

20:41 - December 10, 2015
Lambar Labari: 3461987
Bangaren kasa da kasa, Shahararriyar yar wasan fina-finan Hollywood idan da ‘yan kungiyar Daesh sun san kur’ani da koyarwarsa da ba su kashe mutane ba.


Kamfanin dillanicn labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Albayan ta kasar haddiyar daular larabawa cewa, Angelina Julia fitacciyar yar wasan fim a cibiyar Hollywood ta bayyana cewa idan da Daesh sun san kur’ani da ba su kashe musulmi da kiristoci da sauran mutane ba.

Ta rubuta a shafinta na Twitter cewa, tana da tabbaci a kan cewa addinin muslunci yana kira ne zuwa ga zaman lafiya da fahimtar juna da yafiya  a tsakanin al’umma.

Dangane da jahilcin yan ta’addan Daesh da kur’ani kuwa ta kawo labarin wani kirista da yan ta’adda suka kama tare da matarsa suna tafiya a cikin mota, inda suka tambaye mijin cewa ko shi musulmi ne? sai amsa da cewa kwarai kuwa, said an ta’addan ya ce da shi ka karanta wani abu daga cikin kur’ani sai ya karanta wani abu daga cikin Injila, sai ya ce da shi to a safka lafiya.

Ta ce wannan ya kara tabbatar da cewa wadannan yan taadda ba su ma san kur’ani ba baki daya, kuma suna kashe mutane a matsayin sun aiki da kur’ani wanda hakan babbar masifa ce ga musulmi.

Angelina Julia ta ce bisa ga abin da ya faru daga wannan kissa za a fahimci cewa lallai yan ta’addan Daesh jahilan addinin muslunci ne na hakika.

3461930

Abubuwan Da Ya Shafa: amurka
captcha