Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alalam cewa, sojojin Najeriya sun kai hari a husainiyar Bakiyyatullah, kamar yadda harkar muslunci a Najeriya karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaky ta karyata bayanin da sojoji sika bayar da ke cewa sun kai hari kan babban hafsan hafsoshin sojin kasar a Zariya.
Shafin yanar gizo na harkar 'yan uwa musulmi ya karyata bayanin da sojojin suka bayar, da ke cewa 'yan uwa musulmi sun hana babban hafsan sojojin Najeriya Janar Tukur Yusuf Burutai a lokacin da yake shirin wucewa ta wurin da suka kafa shingaye, inda bayanin ya ce taro ne za a gudanar na saka tuta a babban markazin Husainiyya Bakiyyatullah, amma tun kafin lokacin an jibge sojoji da makamai a wurin, daga bisani kuma suka kai farmaki tare da kashe wani adadi daga cikinsu.
Sai dai anasu bangaren sojojin Najeriya sun ce suna gudanar da taro ne wanda babban hafsan ahfsoshin sojin kasar zai halarta, kuma an dauki matakai na kare lafiyarsa a lokacin da 'yan uwa musulmin suka tare hanyoyi tare da hana shi wucewa a cewar bayanin sojojin.
Haka nan kuma shafin 'yan uwa musulmin ya karyata rahoton da wasu kafofin yada labarai na turai suka bayar da ke cewa babban hafsan hafsoshin sojin na Najeriya ya tsallake rijiya ta baya a Zariya, a lokacin da suka yi masa kwanton bauna.
Hare-haren wuce gona da iri da sojojin gwamnatin Nigeriya suka kai kan gidan shugaban Harkar Musulunci a Nigeriya Sheikh Yakub Ibrahim El-Zakzaki ya janyo hasarar rayuka da na dukiyoyi.
Tun daga jiya Asabar ce sojojin gwamnatin Nigeriya suka fara farma magoya bayan Sheikh Yakub Ibrahim El-Zakzaki kan zargin tsare hanya a daidai lokacin da babban hafsan hafsoshin rundunar sojin kasar ke shigewa a lokacin da magoya bayan Sheikh El-Zakzakin ke shirye-shiryen isa cibiyar gudanar da harkokin addini ta Husainiyyatu Baqiyyatullahi a garin Zariya.
Inda sojojin suka kashe mutane akalla dari daya tare da jikkata wasu da dama, sannan a safiyar yau Lahadi sojojin kasar ta Nigeriya sun sake kai farmaki kan cibiyar gudanar da harkokin na addini ta Husainiyyatu –Baqiyyatullahi tare da rusa ta, sannan suka nausa zuwa gidan Sheikh El-Zakzaki, inda suka lalata wani bangaren gidan.
Rahotonni suna bayyana cewa; Hare-haren sojojin gwamnatin Nigeriya kan cibiyar Husainiyya –Baqiyyatullahi da gidan Sheikh Ibrahim Yakub El-Zakzaki sun lashe rayukan mutane da dama da ba a kai ga tantance yawansu ba, tare da jikkata wasu adadi.
3462830