IQNA

Daruruwan ‘Yan Dagistan Sun Shiga Cikin Kungiyar Daesh

23:10 - December 24, 2015
Lambar Labari: 3469041
Bangaren kasa da kasa, daruruwan ‘yan jamhuriyar Dagistan ne suka tafi yankin gabas ta tsaiya tare da hadewa da kungiyar ta’addancin ta daesh a yankin.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Tashar Alalam cewa, Ramadan Abd Latibov shugaban jamhuriyar Dagistan ya bayyana cewa akwai daruruwan ‘yan jamhuriyar Dagistan kimanin 634 da suka tafi yankin gabas ta tsaiya tare da hadewa da kungiyar ta’addancin ta daesh a yankin domin yaki a cikin sahunsu.



Ya ce yanzu haka an kafa kwamiti wanda ke bin kadun wannan lamari, domin tabbatar da cewa an dakie yunkurin masu gurbata akidar matasa suna kwadaita musu shiga kungiyoyin yan ta’addan da sunan addini.



Hakan ya hada da hudubobin da malamai suke gabatarwa da kuma masana gami da limaman masallatai, domin yaki da irin wannan akida ta ta’addanci wadda ake yadawa a duniya.



Tun kafin wannan lokacin dai shugaban na Dagistan ya sanar da cewa akwai mutanen yankinsa kimanin 300 a cikin kungiyoyin yan ta’adda ayankin gabas ta tsakiya, kafin daga bisani adadin ya karu.



3468991

Abubuwan Da Ya Shafa: daesh
captcha