IQNA

An Tarjama Kur’ani Da Harshen Rashanci A Masar

23:25 - December 26, 2015
Lambar Labari: 3469683
Bangaren kasa da kasa, an tarjama kur’ani mai tsarkia cikin harshen rashanci wanda ma’aikatar harkokin addini ta kasar Masar ta dauki nauyinsa.


Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na veto cewa, an tarjama wannan kur’ania a cikin harshen rashanci bisa himmar masu bncike da kuma masana na kasar Masar.



Wannan tarjama ta cika adadin kur’anai da aka tarjama karkashin wannan ma’aiakat da cewa ya kai kur’anai 9 a jumlace.



Kafin wannan lokacin dai ma’aikatar ta bayar da bayanin cewa an tarjama kur’anai da harsunan turanci, Faransanci, Chananci, Koreyanci, Albaniyanci, Jamusaci, Spaniyanci, da kuma Indonesia.



Ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar bababr manufar tarjama wadannan kur’ani a cikin wadannan arsuna ita ce isar da sakon muslunci zuwa sassa na duniya, da kuma yaki da tsatsauran ra’ayi da sunan addini.



Muhammad Mukhtar Juma’a ministan ma’aikatar addini ya bayyana jiya a lokacin ganawa da Rida Abdussalam gwamnan Sharqiyyah, cewa za a ci gaba da mayar da hankali ga wannan aiki da kuma sirar manzo a cikin ahrsunandaban-daban.



3469426

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha