Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Press TV cewa, an gudanar da wannan zanga-zanga nea wasu daga cikin biranan daa suka hada da Bauchi, Yobe da kuma Kano.
Bayanin ya ci gaba da cewa masu zanga-zangar sun daga hotunan sheikh Zakzaky suna masu yin Allawadai da abin da ya faru na kai hari a kan mabiya tafarkin shi’a tare da cin zarafinsu da kuma kisansu.
A kwanakin baya ne dai jami’an sojin najeriya suka kaddamar da farmaki a kan gidan sheikh Zakzaky tare da kame shi da kuma kasha daruruwan mutane da suka samu a wajen gidansa nasa, kamar yadda uma suka kai wani harin Husainiyar Baqiyyatullah a lokacin da suke zaman janazar wani da ya rasa ransa, inda a nan ma suka kasha mutane bakwai.
Tun bayan kai wannan hari kan mabiya tafarkin shi’a tare da kasha adadi mai ywa daga cikinsu da suka hada da yaran Sheikh Zakzaky guda uku, ya zuwa yanzu babu wani cikaken bayani dangane da makomarsa da ma wadanda aka kame a lokacin, amma jami’an soji suna cewa yana nan cikin koshin lafiya.
http://iqna.ir/fa/news/3466382