IQNA

Mutane 13 Sun Rasu A Wani Hari A Wurin karatun Kur’ani A Nangahar

15:53 - January 18, 2016
Lambar Labari: 3480050
Bangaren kasa da kasa, rahotanni daga yankin Nangar na kasar Afghanistan sun ce mutane 13 sun rasu a wurin karatun kur’ani mai tsarki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Russia Today cewa, a wani wurin karatun kur’ani a yankin Jal Abad na kasar Afghanistan an kai harin kunar bakin wake.

Ofishin gwamnan yankin Nangahar ya ce mutane 13 ne suka mutu sakamakon harin, wasu 14 kma suka jikkata.

Kakakin kungiyar Taliban a kasar ya ce ba su da hannu wajen kaddamar da wannan hari nay au a kan wannan wuri.

An bayyana cewa wanda ya kai harin ya yi jigidar bam ne ya kuma shiga tare da Ataullah Khugyani a wurin taron karatu a gidan da aka gudanar da shin a Abid Shinvari daya daga cikin manyan yan siyasar kasar, kuma wanda ya kai harin dan daesh ne kungiyar ta’addanci.

Wannan dan siyasar Shinvari dai gidansa yana yankin Jalal Abad ne babban birnin lardin Nangahar, wanda kuma hakan yana daya daga cikin ayyukan ta’addanci da kasar take fuskanta  akowane lokaci.

3468222

captcha