IQNA

Azhar Ta Janye Karar Da Ta Shigar Kan Mai Tozarta Kur’ani

22:37 - January 20, 2016
Lambar Labari: 3480060
Bangaren kasa da kasa, cibiyar Azhar ta janye karar da ta shigar a kan mawaki Sha’aban Abdulrahim kan zarginsa da tozarta kur’ani mai tsarki.

Kamfanin dillanicin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Russia Today cewa, Ahmad Tayyib babban malamin cibiyar Azahar ya janye karar da cibiyar ta shigar kan Sha’aban Abdulrahim mawakin kasar ta Masar wanda cibiyar ta zarge shi da tozarta kur’ani.

Ahmad Tayyib ya bayyana cewa wannan mawaki ya gabatar da uzurinsa dangane da abin da ya furta wanda ake kallonsa a matsayin tozarta kur’ani.

Ya kara da cewa abin da wannan mutum ya yi aiki ne na kure kuma an yi masa afuwa kan hakan.

A cikin kwanakin nan ne aka nuna Sha’abn a cikin wani faifan bidiyo da aka watsa ayuotube yana yin izgili da rawanin malaman cibiyar Azharm yana karatun kur’ani da sautin Khalid Tablawi fitaccen makarancin kur’ani na kasar ta Masar.

Baya yada wannan faifan bidiyo cibiyar Azahar ta shigar da kara a kan Sha’abula a gaban kotu, bisa zarginsa da cin zarafin addini da wulakanta karatun kur’ani, a kan haka kotu ta gayyace shi kuma ta yi masa tambayoyi.

Kotun birnin Alkahira ta bayar da belin na Sha’abla akan kudi da suka kai Lira dubu 10, inda aka sake shi.

3468937

captcha