IQNA

Azhar Ta Sanar Da Janye Gasar Da Ta Shirya Domin Kyamar Mazhabar Shi’a

18:14 - January 28, 2016
Lambar Labari: 3480087
Azhar Ta Sanar Da Janye Gasar Da Ta Shirya Domin Kyamar Mazhabar Shi’a
Bangaren kasa da kasa, cibiyar kula da ayyukan mabiya mazhabar shi’a aIraki ta sanar da cewa Azahar ta janye gasar da ta shirya kan kalubalantar shi’a.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na mujaz Irak cewa, babbar cibiyar kula da ayyukan mabiya mazhabar shi’a  aIraki ta sanar da cewa Azahar ta janye gasar da ta shirya kan kalubalantar shi’a a cikin mabiya tafarkin Sunnah.

Matakin janye gudanar da wannan gasa ya zo ne bayan ganawa Tsakanin Ahmad Tayyib da kuma jakadan kasar Iraki a Masar.

Azahar ta bayyana cewa ta dauki wannan matakin ne saboda tana son hadin kai a tsakanin dukkanin al’ummar musulmi, kuma duk abin da zai kawo rarraba tsakanin musulmi ya kamata a kauce masa.

Tun a kwanakin baya ne cibiyar ta sanar da wata gasa mai take hadarin yadwar shi’a a ttsakanin yan ahlu sunna, da kuma hanyoyin da za a bi domin hana ci gaban hakan.

Kamar yadda kuma ta sanar da cewa za ta bayar da kyauta ta kudi lakadan ga duk wadanda suka shiga gasar da kuma wadanda suka nuna kwazo musamman.


3470960 

captcha