IQNA

An Hana Saka Littafan ‘Yan Kungiyar Ikhwan A Baje Kolin Littafai Na Alkahira

22:17 - February 01, 2016
Lambar Labari: 3480101
Bangaren kasa da kasa, an hana a gabatar da littafan ‘yan kungiyar Ikhwan a kasar a baje kolin litatfai na duniya wanda ake gudanarwa abirnin Alkahira.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadawa na yanar gizo na jaridar Qods Alarabi cewa, mahkuntan Masar sun hana a gabatar da littafan ‘yan kungiyar Ikhwan a baje kolin litatfai na duniya wanda ake gudanarwa a birnin Alkahira tare da halaratar madaba’antu.

A lokacin da yake ganawa da wasu daga cikin masu halartar wurin Sharif Ismail firayi ministan kasar Masar ya bayyana cewa, an dauki mataki tantance masu gabatar da littafansu a wannan wuri, kuma ba za a bar wasu su kawo littafansu ba.

Ya ce kungiyar yan uwa musulmi na daga cikin wadanda ba za  abari su baje littafansu a wannan wuri ba, domin kuwa an abukatar littafai ne wadanda za su taimaka wajen samun hadin kai da zaman lafiya a duniya.

Wannan mataki dai bai yi wa da dama daga cikin mabiya wannan kungiya dadi ba, domin kuwa tun tsawon shekaru da kungiyar take shiga wannan baje koli ba a taba hana baje littafanta ba.

Wasu daga cikin daliban jami’oi na kasar ta Masar da suka je wurin sun ce wannan abin ban dariya da kuma kunya ga mahukuntan kasar ta Masar, domin kuwa hana baje littafan ikhwan ba zai hana su samun karbuwa ba.

Daga karshe dai an bayyana cewa kungiyar tana a matsayin haramtatta ne, kuma duk wani abu nata ko da aka dangata da ita ya haramta a hukumancea  kasar ta Masar.

3472031

captcha