
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar The Nation cewa, daruruwan mata musulmi ne suka gudanar da gangamin na ranar Hijabi ta duniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa matan sun cika tituna inda suke nuna rashin amincewarsu da duk wani hankoro na takura ma mata musulmi da ake a wasu daga cikin kasashen daban-daban.
Hafsa Badaru daya daga cikin wadanda suka shirya gudanar da wanann gangami ta bayyana cewa, sun yi hakan ne a matsayinsu na mata masu kishin addininsu da koyarwarsa.
Ta kara da cewa sun jima suna jin yadda ake cin zarafin mata akasashen duniya saboda saka hijabin muslunci, wanda hakan abin yin Allawadai da kakausar murya.
Kamar yadda kuma ta bukaci wasu daga cikin kasashen Afirka da suke tunanin daukar wannan tabia da su canja shawara, doin yin hakan ya yi hannu da demokradiyya.
Yin hakana cewarta mulki ne na kama da danne hakkokin wasu mutane saboda addininsu, tare da yin hannunka mai sanda ga mahukuntan Najeriya wadanda suke tunanin yin hakan bisa hujjar yaki da ta’addanci.
Daga cikin matan akwai wadanda suka daga kwalaye da aka yi rubutu a kansu da ke nuna goyon bayansu ga mata masu saka hijabia koina cikin fadin duniya.
Hakan nan kuma an rufe taron da yin kira ga sauran mata musulmi a dukaknin jahohin kasar da su ci gaba da raya wanann rana ta hijibi ta duniya kamar yadda takwarorinsu suke a koina cikin fadin duniya.