
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Saumariyyah News cewa, Al-fahdawi ya ce wannan shi ne karon farko da ake gudanar da sallar juma’a da hadin kai tsakanin sunna da shi’a a Ramadi tare da halartar manyan jami’a da shgabnannin kabilu bayan yantar da ita daga Daesh da suka mamaye yankin a lokutan baya.
Ya ce an gudanar da wannan salla ne a bababn masallacin Juma’a na birnin Ramadi da ke tsakiyar birnin.
Birgediya Janar Yahya Rasul kakakin dakarun da aka kafa domin yaki da ‘yan ta’adda a Ramadi ya bayyana cewa, an kwato biurnin ne a ranar 28 ga watan Disamban shekara ta 2015, wanda yanzu kuma yana karkashin kulawar jama’a da jami’an tsaro.