IQNA

An Yi Kira Ga Gwamnatin Mauritaniya Dangane Da Bude Makarantun Kur’ani

22:44 - February 07, 2016
Lambar Labari: 3480120
Bangaren kasa da kasa, limamin jum’a na garin Ni’amah ya yi kira ga mahukuntan kasar Mauritaniya kan su taka rawa wajen ganin an bude makarantun kur’ani na warsh a garuruwan Jikni da Kubani da aka rufe.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-siraj cewa, Sheikh Muhammad Amin Wuld talib Yusuf limamin masallacin garin Al-ni’imah ya yi kira da bababr murya ga mahukuntan kasar da su taka rawa wajen janye takunkumin da aka dorawa makarantun kur’ani.

Bayanin ya ci gaba da cewa shehin malamin ya bayyana wanann mataki na rufe makarantun kur’ani mai tsarki da ake tafiyar da su bisa tsohon tsari da cewa, hakan ba adalci ba ne ga wadanda suke yi karatun, wadanda su ma yan kasa ne kamar kowa.

Limamin ya ce yana kira kira ga shugaba Muhammad Wuld Bin Abdulaziz da cewa, ya a iye batun babu ruwansa da tsarin addini ya yi wa wadannan bayi Allah adalci, wadanda suke karatun kur’ani mai tsarki ba tare da wani tattallafi daga gwamnati ba.

A lokutan baya ne dai mahukuntan kasar ta Mauritaniya suka sanar da rufe wasu makarantun kur’ani mai tsarki, bisa hujjar cewa bas u da rijista, daga bisani kuma aka ce ana shakku kan hanyoyin da suke samun kudade da ake tafiyar da su, wanda hakan yasa har yanzu suk eci gaba da kasancewa a rufe.

3473325

captcha