IQNA

An Bayar Da Kyutar Kur’anai Da Littafan Addini Ga Masallatan Afirka Ta Kudu

22:21 - February 10, 2016
Lambar Labari: 3480126
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin daliban kasar Somalia kasar Afirka ta kudu sun bayar da kyautar kwafin kur’anai da littafan addini ga masallatan birnin Cape town.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ishahid.net cewa, daliban kasar Somalia kasar Afirka ta kudu sun bayar da kyautar kwafin kur’anai da littafan addini ga limaman masallatan yan Somalia a birnin Cape town na kasar.

A wuron an samu halartar manyan mutane yan kasar ta Somalia da suke gudanar da harkokinsu musamman na addini da jagorancin cibiyoyi da ke yada muslunci a kasar.

Sharmaki Mu’allim Hamza shugaban kungiyar daliban jami’a yan kasar Somalia a kasar Afirka ta kudu ya bayyana a wajen taron cewa, dukkanin littafan da aka bayar, kokari ne na daliban kasar Somalia, da nufin karfafa musulmi da kuma raya dakunan karatu na masallatai.

Abin tuni a nan dais hi ne, yan kasar Somalia mazauna kasar Afirka ta kudu suna taka gagarumar rawa a bangarorin kasuwanci da saransu a kasar.

3474283
captcha