IQNA

An Bude Wani Taron Karatun Kur'ani A Kasar Mauritaniya

22:42 - February 13, 2016
Lambar Labari: 3480135
Bangaren kasa da kasa, an bue wani taron karatun kur'anin mai tsarki tare da halartar makaranta 60 mai take goyon baya ga manzon Allah (SAW) a birnin Nuwakshot fadar mulkin kasar Mauritaniya.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na aqlame.com cewa, a jiya ne aka bude zaman taron karatun kur'ani mai tsarki mai taken taimakon Allah da manzonsa (SAW) a otel na Khater a birnin Nuwakshot.

Sheikh Ali Rida bin Muhammad Naj Alsu'aidi shugaban cibiyar kula da ayyukan kur'ani mai tsarki ta taimakon Allah da Manzo (SAW) shi ne ya jagoranci bude taron, inda Sayyid Muhammad bin Mahmud bin Badi ya gabatar da jawabi ga mahalarta taron.

Inda y ace kur'ani yana koyar da dan adam abubuwa da dama da suka hada da hakuri, gidun duniya, hakuri, godiya, kaunar juna, fata, tsoro, dogaro da Allah, yarda da Allah da abin da ya kaddara.

Bayanin ya ci gaba da cewa babar manufar gudanar da wannan taron karatun kur'ani mai tsarki ita ce tunatar da musulmi dangane da koyarwar wannan littafi mai girma, wanda Allah ya safkar ga manzonsa domin ya zama jagora da shiriya ga bil adama baki daya.

Bayan karatun kur'ani an gabatar da wakokin yabon manzon Allah (SAW) a wurin, kamar yadda kuma wasu malaman suka gabatar da jawabai na fadakarwa ga malarta taron.

Tashar talabijin ta Alhurra ta watsa wannan taro kai tsaye a lokacin da ake gabatar da shi daga birnin Nowakshot.

3475151
captcha