
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na Miknas Press cewa, babbar manufar wannan cibiya da ake shiriya samarwa ita ce ita hada fahimta wuri guda domin fitar da abin da zai amfani al’umma, inda babbar ranar tarukan za ta 14,15 da 16 ga Afirilun 2017.
Bayanin ya ci gaba da cewa a cikin wannan shiri za a yi kokari matuka domin bayar da dama ga dukkanin bangarori na musulmi domin su bayyana mahangarsu a kan lamurra da dama da suka shafi addini, domin samun hadin kai da fahimtar juna atsakanin musulmi.
Kamar yadda kuma za a rika karbar makaloli na da suka danganci ilmomin kur’ani ko na wasu bangarori na addini a daidai mahanga da fahimtar marubuci daga kowane bangare na muuslmi, domin samar da abu guda wanda aka amince da shi baki daya.
Haka nan kuma wanann shiri zai zama shi ne irinsa na farko wanda babbar cibiyar za ta dauki nauyin gudanarwa tare da hadin gwaiwa da wasu kungiyoyi da cibiyoyi na kasa da kasa, inda kuma za a rika karbar bayanai da rubuce-rubucen makaloli daga musulmi daga dukkanin bangarorin duniya kafin lokacin gudamar da bababn zaman.
Za a sanar sanar da lokacin bayar da sakamakon makalolin da aka rubuta, kuma za a iya tuntubar babban ofishin kula da ayyukan cibiyar.
Lambar waya; (212) 5 35 96 28 84
Shafin yanar gizo: : www.mobdii.com
Adireshin Email: : mobdiimotamar3@gmail.com