
Kamfanin dilalncin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Yaum sabi cewa, Sharif Ismail firayi ministan kasar Masar ya kori ministan shari’a saboda yin kalamin batunci ga manzon Allah (SAW) tare da daukar matakan ladabtarwa akansa.
Ahmed al-Zind ya fada a wata muhawara gidan talabijin inda yake mayar da martani kan kama wani Dan Jarida saboda zargin cewar ya bata masa suna, inda ministan yace koda Mazan Allah (SAW) ne zai kama shi.
Babbar cibiyar addini ta Azhar ta yi kakkasar ska kan wannan batu, tare da bayyana cewa matsayin manzo (SAW) ya wuce wasa.
Mista Zind ya yi wannan magana ce a wata hira da gidan talbijin ranar Juma'a.
Sai dai nan da nan ministan ya nemi gafarar Allah da cewa, "Allah na tuba ka yafe mini," kuma ya sake neman afuwa washe garin ranar.
Firai minista Sherif Ismail ne ya sallami minista Zind daga aiki.
Alkalan kasar Masar sun fitar da sanarwa da ke nuna adawa da korar Mista Zind daga aiki, suna masu cewa "abin da yayin ba da gangan ba ne kuskuren harshe ne."
Mista Zind dai ya kasance mai matukar sukar kungiyar 'yan uwa Musulmi ta Muslim Brotherhood.
Furucin dai yana ci gaba da fuskantar kakkausar suka da mayar da martini daga sassa daban-daba na cibiyoyin muslunci a kasar ta Masar da ma sauran kasashen musulmi, tare da yin kira da a dauki kwararan matakai na ladabtarwa a kansa sakamkon yin furuci na batunci ga manzon Allah (ASW)
Kamar yadda kuma wasu suke ganin cewa ya kamat a dauki mataki da ya dace domin hana faruwar irin hakan a kasar ta Masar nan gaba, doin kare martabar manzo.