IQNA

Tashin Bam A Arewa Maso Gabashin Nigeria Ya Lashe Rayuka 22

23:25 - March 16, 2016
Lambar Labari: 3480237
Bangaren kasa da kasa, tashin wasu abubuwa masu tarwatsewa a cikin wani masallaci a kusa da birnin Maidugri na jahar Borno Najeriya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 22 da jikkatar wasu kimanin 18.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin tashar Press TV cewa, rahotanni daga Najeriya na cewa mutane 22 ne suka rasa rayukan su sakamakon wani hari da ake kautata zaton na kunar bakin wake a wani masalaci dake Maiduguri a arewa maso gabashin kasar.

Harin na asubahin yau Laraba wanda ake dangatawa dana kungiyar Boko Haram ne ya kuma yi sanadin jikkatar mutane da dama a cewar wasu majiyoyin asibiti.

Wasu rahotanni sun ce 'yan kunar bakin waken sun shiga masallacin ne na yankin umurari molai da ke Maidugurin, yayin da mutane ke cikin sallah suka dasa bama-baman.

A kwanakin baya ma mayakan Boko Haram sun kai wani haroi a wani kauye da ke tazarar kilo mita 12 daga Maidugri inda suka kashe mutane 85.

Hare-haren Boko Haram a Najeriya sun yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 17 tare da tserewar wasu kimanin miliyan 3 daga gidajensu.

Daga bisani kungiyar ta fadada hare-harenta zuwa kasashe makwabtan Najeriya, wato Kamaru, Chadi, da kuma Nijar.

3483906

captcha