IQNA

Obama: Bata Sunan Musulmi Amfanin ‘Yan Ta’adda Ne

23:34 - March 26, 2016
Lambar Labari: 3480265
Bangaren kasa da kasa, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya bayyana cewa bata sunan musulmi da musulunci amfanin ‘yan ta’adda ne.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakaltoo daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Alalam cewa, a lokacin da yake gabatar da jawabi na mako-mako, Barack Obama ya yi Allawadai da harin da aka kai birnin Brussels na kasar Belgium, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 34 tare da jikkatar wasu kimanin 300, wanda Daesh ta dauki nauyin kai harin.

Obama ya isar da sakon ta’aziyarsa ga iyalan Amurkawa biyu da suka rasa rayukansu a harin, tare da yin fatan samun lafiya ga wasu Amurkawa 14 da suka samu raunuka a harin.

Ya ce ko shakka babu wannan aikin ‘yan ta’adda ne, kuma suna son su tunzura m ne domin mu dauki matakin takura musulmi a kasarmu, ya ce Amurka kasa ce wadda kowa yake da yancin yin addininsa, a kan ya ce ‘yan ta’adda ne suke kokarin bata sunan musulmi da ayyukansu na ta’addanci.

Furucin an Obama dai ya zo a matsayin mayar damartani ga Donal Trump dan takatar shugabancin Amurka, wanda yake kokarin tunzura Amurka kan musulmi bayan kai harin na Brussels.

3484589

captcha