Kamfanin dilalncin labaran iqna ya
nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na National Word cewa, an bude cibiyar
ne tare da halartar shugaban kasar urkiya rajab Tayyib Ardugan wadda fadinta ya
kai hekta 6 tare da halartar wasu turkawan.
Wanann cibiya ta hada bangarori daban-daban da suka hada da makaranta da kuma dakin karatu da masallaci wanda zai ci mutane 1400, da kuma wurare na hutawa.
Ahmad Adik wani malamin jami’a ne wanda yake da hannu a wajen gina wannan babbar cibiya, ya bayyana cewa za su rika daukar dalibai kimanin 350 domin gudanar da yawun bude idi da kuma samun masaniya kan addini.
Wanann cibiya dai tan adaga cikin amnyan cibiyoyi na kasashen turai na musulmi da ake gudanar da ayyukan na yada al’adun muslunci da kuma koyarwarsa gami da ilmominsa.
Aikin gina cibiyar dai ya kebanci musulmi yan kasar Turkiya ne mazauna kasar ta Amurka, amma kuma akwai wasu daga cikin musulmi yan wasu kasashe da suke da hannu wajen bayar da gudunmawa kan lamarin.
Daga cikinsu kuwa akwai yan kasar Pakistan, da kuma wasu kasashen larabawa wadanda su ma sun duk halraci wurin, duk kuwa da cewa shugaban na Turkiya shi ma ya bayar da gudunmawarsa ta hanyar halartar bude cibiyar.
Hakan ya zo kuwa duk da irin tsannaun adawar da wasu daga cikin yan majalisar dokokin Amurka musamman ma yan majalisar dattijai, sun nuna rashin gamsuwarsu da bude wannan cibiya ta musulunci.