IQNA

Taro kari Na 13 Kan Addinin Annabi Ibrahim A Canada

23:38 - April 02, 2016
Lambar Labari: 3480286
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da zaman taro karo na 13 a birnin Peter Boron a kasar Canada kan addinain annabi Ibrahim.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na My Kawartha cewa, an fara gudanar da wannan taro ne tun a cikin shekara ta 2004 bayan kai harin 11 ga watan satumban 2001.

Taron na bana za a gudanar da shi sakamakon harin da aka kai a paris da kuma masallacin Peter Boro wanda duk ya shafi musulmi da ma wadanda ba musulmi ba.

Babbar manufar taron dai it ace girmama matsayin annabi Ibrahim (AS) a matsayinsa na shugaban dukkanin addinai na kiristanci, kiristanci da kuma msulunci.

Baya ga hakan kuma daga cikin manufofin taron har da karfafa tattaunawa atsakanin mabiya addinai da aka safkar daga sama, domin karfafa su wajen samun fahimtar juna da zama lafiya.

Kamar yadda kumav za a gabatr da bayanai dangane da mahangar kur’ani mai tsarki kan dukkanin wadandannan addinai, da kuma yadda yake yin kira zuwa ga zaman lafiya da girmama dana dam, domin kuwa shi kur’ani yana fassara addinin msulunci ne, wanda shi ne zaman lafiya da kwanciyar hakankali bisa fadar ubangiji.

3485146

captcha