IQNA

An Yanke Kudin makarantar Musulmi Mafi Girma A Australia

22:33 - April 04, 2016
Lambar Labari: 3480290
Bangaren kasa da kasa, an yanke kudin makaranta mafi girma ta musulmi a kasar Australia sakamakon wasu matsaloli da aka fuskanta.

Kafanin dillancin lav\baran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na nine News cewa, yanzu an yanke kudin makarantar sarki Fahad mafi girma ta msuulmi a kasar Australia a cikin wannan mako wanda ya kai dala miliyan 20.

Gwamnatin kasar ce ta dauki wannan mataki, saboda abin da ta kira rashin tsari a wajen tafiyar da wannan makaranta ta fuskar gudanarwa da kuma kasafin kundinta, wadda ke da dalibai 2400.

Reck Mitry shi ne lauyan makarantar, ya kuma bayyana cewa za su daga wannan Magana zuwa kotu domin bin kadun lamarin ta hanyar shari’a.

Ya kara da cewa babban abin da ake zargin makaerantar shi ne, it ace makaranta mafi girma ta msuulmi, amma kuma bata da tsari a bangaren gudanar da ayyukanta da kuma yadda take kashe kudi.

Simon Birmingham shi ne ministan ilimi na kasar ta Australia, ya bayyan acewa matukar dai ba a gaggauta warware matsalar kasafin kudin makarantar ba, to wannan mataki zai zaman a dindin.

Mahkntan kasar suna cewa makarantar da take samun kasafin kudinta daga kasar saudiyya, a halin yanzu ba ta samun kudadenta kamar da, kuma ga dalibai da suke karatu a ciki ba su samun kulawa kamar yadda ya kamata, domin suna kokawa.

Ya zuwa yanzu dai kimanin makarantu 6 ne mahukuntan kasar ta Australia ta dauki irin wannan matakia kansu, sakamakon irin wannan matsala ta rashin bin kaida da kuma rashin kiyaye tsari yadda ya kamaya, kamar yadda makarantar ta sarki Fahad take yi.

3485700

captcha