
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gioz na Hindu cewa, wata malamar firamare ta ci zarafin wani dalibinta musulmi a cikin makaranta inda kuma aka bukaci ayi bincike.
Malamar ta yi izgili kan yaron ne a lokacin da aka yi Magana kan ta’addanci, kasantuwr cewa shi kadai ne musulmi a ajin nasu, sai ta mayar da batun a kansa.
Wannan lamari ya bakanta ran mahaifan yaron, inda suka ce ba za su taba yarda da hakan ba, domin kuwa yaronsu yana da takardun zama dan kasar Amrka kamar sauran Amurkawa, saboda haka babu wanda yake da hakkin cin zarafinsa.
Jami’an makarantar sun ce suna bin kadun wannan lamari, kuma yanzu haka an dakatar da wannan malama daga kyawa a wannan makarant, inda suka ce ba za su taba yarda wani ab mai kama da haka ba, kuma ba da yawun akarantar ta yi hakan ba.
Wani mai fafutukar kare hakkin bil adama a jahar Texas ya ce bai kamata a ci zarafin wani mutum ba saboda addininsa ko akidarsa ba.