Kamfanin dillancin labaran iqn aya
nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na CTVNews cewa, an gudanar da wannan
zaman taro ne a matsayin tattaunawa ta addinai da ala’du.
Da dama daga cikin wadanda suka halarci wannan zaman tarin shun nuna jin dadi matuka dangane da jawaban da aka gabatar kan muslunci.
Lauren Cley day ace aga cikin daliban makarantar sakandare a wurin, tana daya daga cikin wadanda suka shirya taro, ta bayyana cewa babban abin da ya sanya su yin hakan shi ne kara kusanto da fahimta a tsakanin jama’a.
Rayan Maggy shi ma yana daga cikin mahalrta taron, ya bayyana cewa sun ji dadi matuka, domin kuwa wanann wani abu e wanda ya hada mutane da suka hadu kan yan adamtaka da fahimtar juna.
Bahati daya daga cikin musulmi maharta wurin ya bayyana cewa, wasu daga cikin yan gudun hijra sun zo wurin kum an taimaka musu, yayin da kuma aka kara bayani ga mahalarta kan yadda suke da mummunar fahimta kan muslunci, cewa bah aka ba ne, yan taadda daban musulmi daban.