
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-siraj cewa, an gudaar da wannan zaman taro ne a birnin Nuwakshot fadar mulkin kasar a jiya.
Bayanin ya ci gaba da cewa ko shakka babu a kowane lokaci ilmomi sai kara bayyana suke yida fito daga cikin kur’ani mai tsarki, wanda kuma ahakan yana daga cikin nauin mujizarsa.
Tarjamar ayoyi ko ma’ana ba wani abu bane illatfasiri, amma mujiza a dukkanin bangarori na kur’ani ba ta da makamanci, domin kuwa shi dukkaninsa mujiza ne.
Ya ci gaba da cewa, musulmi suna koyon ilmominsa kuma suna kowane lokaci suna kara fahimtar cewa kur’ani bai kebantu da wani lokaci banda wani lokaci ba.
Hammud Wuld Amar Judah yan ada cikin wadanda suka gabatar da jawabi a wannanzaman taro, wanda shi ma ya yi ishara zuwa ga wasu muhimamn lamurra da ya kamata masu nazari su mayar da hankalia kansu dangane da kur’ani, musamman ta fuskar mujiza.
Taron dai ya samu halartar makaranta da manazarta na jami’oi gami da kuma malami da suka gabatar da makaloli a wurin.