IQNA

Jagoran Juyin Islama:

Wajibi Ne A Mayar Da Hankali Ga Gina Tattalin Arziki mai Karfi

23:52 - April 07, 2016
Lambar Labari: 3480299
Bangaren siyasa, ya gana da wasu daga cikin 'yan majalisar ministoci, manyan jami'an majalisar shawarar Musulunci, manyan jami'an ma'aikatar shari'a da sauran jami'an cibiyoyi da hukumomi na gwamnatin Iran, inda ya jinjin kan ayyukansu da kuma yi musu hannunka mai sanda kana bin da ya kamaa a mayar da hankali na gina tatatlin arziki da hidima ga al’aumma.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin jagora cewa, a yau Laraba (06-04-2016) ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da wasu daga cikin 'yan majalisar ministoci, manyan jami'an majalisar shawarar Musulunci, manyan jami'an ma'aikatar shari'a da sauran jami'an cibiyoyi da hukumomi na gwamnatin Iran inda yayin da yake mika godiyarsa ga jami'an musamman jami'an bangaren gudanarwa saboda kokarin da suka yi wajen ci gaba da bin diddigin siyasar tabbatar da tattalin arziki na dogaro da kai, inda ya bayyana cewa tabbatar da hadin kai da aiki tare tsakanin dukkanin bangarori na gwamnati wani lamari ne mai matukar muhimmanci wajen aiwatar da wannan siyasa ta tabbatar da tattalin arziki na dogaro da kai.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Wajibi ne gwamnati musamman shi kansa mataimakin shugaban kasa ya zamanto shi ne mai jagorantar wannan cibiya ta tabbatar da siyasar tattalin arziki na dogaro da kai din. Sannan kuma ta hanyar aiki tare da kuma taimakon dukkanin cibiyoyin na kasa za a sami gudanar da aikin da ya dace wajen zaburar da bangarori daban-daban da kuma karfafa kayayyakin da ake samarwa a cikin gida.

Jagoran ya bayyana irin rawar da cibiyar tabbatar da tattalin arzikin dogaro da kai za ta taka wajen sanya ido kan ayyukan cibiyoyi na gwamnati a matsayin wani lamari mai matukar muhimmanci inda ya ce: A saboda haka wajibi ne a karfafa cibiyoyin da suke gudanar da ayyukansu karkashin wannan siyasar, sannan sauran cibiyoyin 'yan ba ruwanmu ma, wajibi ne a janyo hankalinsu, kana kuma a dau matakan da suka dace a kan cibiyoyin da suke aiwatar da abin da ya saba wa wannan siyasar da kuma hana su yin hakan.

Haka nan kuma yayin da yake bayanin cewa wajibi ne aiki da za a gudanar a fagen karfafa tatttalin arziki na dogaro da kai ya zamanto ta yadda a karshen shekara za a iya gabatar da wani rahoto kan ayyukan da aka gudanar wadanda kuma za a gansu a kas a bangarori daban-daban, Jagoran ya bayyana cewar: Cibiyoyin gudanarwa suna da karfin tabbatar da wannan siyasa ta tattalin arzikin dogaro da kai. Don haka wajibi ne majalisar shawarar Musulunci ta taimaka wa gwamnati a wannan bangaren.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Ni dai ba ina son daga irin fatan da mutane suke da shi ba ne, kamar yadda kuma ina da masaniya dangane da irin matsaloli da rashin da muke da shi, to amma wajibi ne a yi amfani da hanyar tsumulmular wasu abubuwan da muke da su don cike gibi da rashin da ake da su a wasu bangarorin.

Jagoran ya bayyana jami'an gudanarwa da ake da su a kasar Iran da cewa jami'ai ne masu kwarewa wadanda kuma suke da tunani da kuma son aiki don haka sai ya ce: Wajibi ne cibiyar gudanarwa ta yi amfani da irin kwarewa ta gudanarwa da ake da ita a kasar nan bugu da kari kuma kan irin fagagen da ake da su na aiki a cibiyoyi daban-daban wajen bin diddigin ayyukan da aka sa a gaba.

Har ila yau kuma yayin da yake bayanin cewa gudanar da kasa wanda aiki ne da ke wuyan gwamnati da kuma shi kansa shugaban kasa mai girma wani aiki ne mai wahalar gaske, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Bisa la'akari da ayyuka masu yawa da kuma fadi da suke kan shugaban kasa, don haka mataimakin shugaban kasa wanda shi ma wani mukami ne mai girma, zai iya taka wata gagarumar rawa wajen gudanar da ayyukan tabbatar da tattalin arziki na dogaro da kai.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Ni dai ina goyon bayan duk wani aiki da kokari da za a ci a bangaren gwamnati, majalisar da kuma ma'aikatar shari'a da nufin kyautata rayuwar mutane da magance matsalolin da ake fuskanta, to amma abin da ke da muhimmanci shi ne tabbatar da cewa aikin da ake yi din wani aiki ne mai amfani ga kasa sannan kuma wajibi ne a yi shi.

Jagoran ya jaddada cewar: Wajibi ne a dogara da irin karfi da kuma albarkatun da ake da su a cikin gida yayin gudanar da siyasar tattalin arziki na dogaro da kai.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana Amurka a matsayin babbar alama ta munanan ayyuka a duniya inda ya ce: Lalle Amurka ba abar yarda ba ce. Ba ya ga Amurkan ma akwai wasu kasashen Yammacin wadanda su ma haka suke. A saboda haka wajibi ne mu dogara da irin karfin da muke da shi. Matsaya da kuma ayyukan jami'an Amurka kuwa suna kara tabbatar da wannan maganar.

Ayatullah Khamenei ya jaddada cewar matukar dai muka shigo cikin fage da dukkan karfi da kuma gaskiyarmu, ko shakka babu Allah Madaukakin Sarki zai taimaka mana. Jagoran ya ci gaba da cewa: A rayuwa ta daidaiku da ta zamantakewa ta al'umma a koda yaushe akan fuskanci matsaloli da wahalhalu, to amma abin da ke da muhimmanci shi ne kada a mance da tafarkin da ake kai duk kuwa da irin wadannan matsalolin da ake fuskanta din.

Har ila yau kuma Jagoran ya sake jaddada wajibcin ba da muhimmanci ga abubuwan da ake samarwa a cikin gida da kuma batun tabbatar da hadin kai da aiki tare tsakanin jami'an bangarori daban daban na gwamnati don ciyar da kasa gaba.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: A koda yaushe Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kasance tana karkashin hadin kai na kasa, to amma a bangare guda kuma wajibi ne a samar da yanayi na hadin kai da fahimtar juna da kuma aiki tare tsakanin gwamnati, duk kuwa da cewa hakan ba wai yana hannun riga ne da bambanci na siyasa da salon gudanarwa tsakaninsu ba.

Jagoran ya bayyana wannan ganawar a matsayin wata alama ta hadin kai da aiki tare tsakanin jami'an gwamnati inda ya ce: wajibi ne dukkanin jami'an gwamnati, duk kuwa da bambanci na siyasa da mahanga da suke da shi, su yi aiki tare wajen ciyar da manyan manufofin juyin juya halin Musulunci.

A wani bangare na jawabin nasa, Ayatullah ya bayyana godiyarsa maras iyaka ga iyalan jami'an gwamnati musamman matayensu saboda hakurin da suke nunawa inda ya ce: Ko shakka babu matayen da dama daga cikin jami'an gwamnati suna da hannu cikin irin kokari da aiki tukurun da jami'an suke yi, wanda ba kasafai ake la'akari da hakan ba.

Har ila yau a yayin wannan ganawar, mataimakin shugaban kasar ta Iran Malam Ishaq Jihangiri ya gabatar da jawabinsa inda ya gode wa Jagoran juyin juya halin Musulunci saboda irin shawarwari da kuma goyon bayan da yake ba wa gwamnatin ta su inda ya bayyana irin ayyukan da gwamnatin ta yi sannan kuma take ci gaba da yi wajen ciyar da kasar Iran gaba musamman ma wannan siyasa ta tattalin arziki na dogaro da kai.

Daga karshe dai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jagoranci jami'an gwamnatin sallar azahar da la'asar.

3486472

captcha