IQNA

Taro Kan lamurra da Suka Shafi Kur’ani A London

22:07 - April 09, 2016
Lambar Labari: 3480308
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zaman tar a birnin London dangane da lamurra da suka shafi kur’ni da kuma yadda za a kara kyautata su.
Kamfanin dilalncin labaran kur’ani na Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na QAF cewa, wannan shiri ana gudanar da shi ne karkashin kulawar cibiyar da ke kula da hubbaren Abul Fadl Abbas (AS) a ofishin cibiyar Nur da ke Landan.

Manufar taron dai ita ce hada malamai masu koyar da karatu da sauran ilmomin kur’ani mai tsarki kan wani tsari guda na koyarwa.

Babban malami sheikh Diya Zubaidi shi ne shugaban wannan cibiya da take da alaka da cibiyar hubbaren Abbas (AS).

Dukkanin mahalarta wannan taro dai sun hadu a kan wajabcin mayar da hankali matuka wajen ganin an kyautata tsarin koyar da karatun kur’ani mai tsarkia makarantun muslunci, domin samar da al’umma masaniya kan kur’ani mai tsarki da kuma ilmominsa.

3486970

captcha