
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Newshub cewa, daki na farko na shiga wannan wuri yana da alaka ne da babban masallacin Qirawan na tarihi, wanda masu zuwa kallo suke faraway da shi.
Haka nan kuma wurin yana da wani daki da aka kebance na jiye tsoffin kudade da aka yi amfani da su a tarihi, da wasu ababen ajiye ruwa na da.
Sai kuma wani daki da aka kira dakin kur’ani mai tsarki, wanda aka ajiye kwafin kur’ani mai tsarki na zamanin da a wannan wuri.
An kuma a jiye wasu daga abubuwan mmatukar muhimamnci na tarihi kamar haka:
Kwafin hoton babban masallacin Qirawan
Wani kasko daka yi kawanya da launi kore
Wani abin shan ruwa da ke komawa zamanin Khalifofin Fatimiyyah
Haka nan kuma akwai kawafin kur’anai da aka rubuta na daruruwan shekaru da ska gabata, wanda daga cikinsu akwai wanda aka rubnuta a cikin karni na tara, kuma kimarsa zata kai Yuro dubu 300.
Kur’ani da rubutun Hijaz da aka rubuta a Qirawan a karni na 8
Abin duba rana na karni na 9