IQNA

Ana Farautar Wani Mutum Da Ya Kai Hari Kan Makarantar Musulmi A Sweden

19:25 - April 11, 2016
Lambar Labari: 3480313
Bangaren kasa da kasa, Jami'an 'yan sanda na farautar wanu mutum da ya kai hari a jiya a kan wata makarantar muuslmi a garin malmo da ke kudancin kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin yada labarai na Evenin Standard ya bayar da rahoton cewa, Cliss Wenson kakakin rundunar 'yan sanda na birnin malmo ya sheda wa manema labarai cewa, suna cikin farautar mutumin da ya kai hari kan wannan makarata ta musulmi.


Bayanin ya ce bayan da aka cinna wuta kan wannan makaranta, 'yan sanda sun ga wani mutum a lokacin yana tsrewa daga wurin a cikin wata mota, kuma sun bi shi amma yaki tsayawa, kuma daga bisani ya tsere musu, duk kuwa da cewa su yi ta yin harbi da bindiga domin tsayar da shi.

A cikin makonni da suka gabata an kai hare-hare a kan makarantun mabiya addinin muslunci a garuruwa daban-daban na kasar ta Sweden, da ma wasu cibiyoyin addini na musulmi, kamar yadda aka kai wasu hare-hare kan sansanonin 'yan guun hijira, wadanda akasarinsu musulmi ne.

3487328

captcha