Kamfanin dillancin labaran iqna ya
habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na innfrad.com cewa, ma’aikatar kula
da harkokin addini ta kasar Kuwait ta zabi gidan radiyon kur’ani na kasar Masar
a matsayin wanda ya lashe kyautarta da ban girma.
Za a bayar da kyauta girmama wag a wannan gidan radiyo a ranar Laraba mai zuwa a taron gasar kur’ani da a za a gudanar a ginin Crown Palaza da ke kasar ta Kuwait.
Wannan gidan radiyo dai ya fara gudanar da shirinsa tun daga ranar 29 ga watan Maris na shekara ta 1964, inda manyan makaranta kur’ani na duniya da suka fio daga Masar suka fara yin karatua acikinsa, da suka hada da Sheikh abdulbasit Abdulsamad, Sheikh Musatafa Isma’il, da sheikh Muhammad Ref’at.
Haka nan kuam radiyo kur’an na kasar masar na daga cikin fitattun gidajen radiyo a kasar, kuma shi ne radiyon kur’ani na daya a duniya.