IQNA

An Samu Gawawwakin ‘Yan shi’a 350 A Najeriya

21:29 - April 13, 2016
Lambar Labari: 3480318
Bangaren kasa da kasa, an samu gawawwakin mabiya mazhabar shi’a 350 da aka kasha a Husainiyar Baqiyatullah a Zaria Najeria.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na Alalam cewa, Muhammad Namadi Musa ya sheda cewa an samu wadannan gawawwaki ne daga cikin mutanen da sjojin najeriya suka kasha, kuma yanzu haka akwai mutane daga 300 har zuwa 730 da ba a san makomarsu ba.

A nata bangaren Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa ta bukaci sojojin Najeriya su yi bayani kan kisan gillar da aka yi a Zaria a kan mabiya mazhabar shi'a.

Babban daraktan kungiyar a reshenta da ke Najeriya ne ya sanar da hakan, inda ya bayyana cewa bayanan da gwamnatin Kaduna ta bayar kan cewa sojoji sun bizne mabiya mazhabar shi'a 350 a wani makeken kabari guda daya a lokaci guda, ya sanya dole ne sojoji su yi bayani kan wadanda suka aikata wannan ta'asa daga cikinsu.

Kungiyar ta ce abin da ya faru yana da matukar sosai rai, kuma tana ci gaba da harhada bayanai kan hakikanin abin da ya faru, wanda za ta fitar nan ba da jimawa ba.

Yanzu haka a nata bangaren kotun manyan laifuka ta duniya tana harhada bayanai kan abin da ya faru na kisan gilla kan mabiya mazhabar shi'a a Zaria, bayan da wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama masu zaman kansu suka shigar da kara a kan gwamnatin Najeriya da rundunar sojin kasar kan wannan lamari, wanda shi ma bayan kammala bincike daga bangaren kotun manyan laifuka ta duniya kan lamarin, za ta sanar da mataki na gaba ta fuskar sharia'a.

Wannan lamari dai ya saka gwamnatin najeriya cikin mawuyacin hali, domin kuwa bayan faruwar lamarin ta yi kokarin kare kanta, amma hakan bai yiwu ba, saboda hujjojin da suka bayyana kuma suke ci gaba da bayyana kan cewa sojojin kasar sun yi kisan kiyashi kan mabiya mazhabar shi’a marassa makami.

3488164

captcha