IQNA

Makarantan Kasar Iran Na Halartar Gasar Kur’ani A Kuwait

23:47 - April 14, 2016
Lambar Labari: 3480323
Bangaren kasa da kasa, an kammala tantance makarancin kur’ani na kasar Iran a gasar da aka fara a kasar Kuwait a jiya.

Kamfanin dillancin labaran Kur’ani Iqna ya habarta cewa an bude taron gasar ne ta kasa da kasa ajiya tare da halartar Sabah Khali hamad sabah, mataimkain firayi ministan kasar ta Kuwait.

Bayanin ya ci gaba da cewa an tantance makaranta da kuma bangarorin da za su gudanar da gasa a kansa a lokacin budewar.

Ibrahim Fallah Tabassom Chehreh makarancin kur’ani daga jamhuriyar muslunci ta Iran an tantance shi, kuma an bashi bayanin dukaknin bangarirori da kuma lokuta da zai gabatar da gasar.

Shi ma a nasa bangaren Mahammad Mahmudi mahardacin dukkanin kur’ani daga kasar Iran, an bashi bayanin gasar da zai gudanar lokuta da rana kamar yadda yake bisa kaida.

Wanna dais hi ne karo na 7 da ake gudanar da wannan gasa ta kasa da kasa akasar Kuwait, wadda daga karshe za a bayar da kayutuka ga wadanda suka nuna kwazo, tare da halartar bikin rufe gasar daga manyan jami’an gwamnatin kasar, da suka hada da Sabah Ahmad Jabir Al-sabah, sarkin kasar.

3488547

captcha