Kamfanin dillancin labaran iqna ya
ahbarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-siraj cewa, a
ne aka fara gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta Maher a
kasar Mauritaniya a birnin Nuwakshot tare da halaratr wasu jami’ai.
Wadanda suka samu halartar wanann gasa ta maher a kasar mauritaniya a cikinsu ne za a fitar da wasu wadanda suka fi nuna kwazo domin su samu damar halartar bababr gasar hadar kur’ania birnin makka na kasar Saudiyya.
Wuld Sidi Abdulkadir shi ne shugaban kwamitin shirya gasar kur’ani a kasar mauritaniya, ya kasance tare da manyan jami’ai na kasar wajen bude wannan gasa.
Abu Mus’ab Muhammad almuzhar shi ne manzon musamman na kungiyar shirya gasar kur’ani ta duniya, wanda ya halarci bude wannan gasa, inda ya gabatar da jawabi ga mahalarta taron, da suka hada da jami’a da malamai da kuma daruruwan daliban kur’ani.
Wannan gasa dai tana daya daga cikin wadanda ke gudanarwa irinta masu matukar muhimamnci a kasar ta Mauritaniya, domin kuwa tan amatsayin babbar dama ga dukaknin wadnda suka samu nasara, domin zuwa gasar kur’ani ta duniya a kasashe daban-daban.