Kamfanin dillancin labaran kur’ani na Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na Veto cewa, an watsa hotna na wani wani kwafin kur’ani mai tsarki da aka gano mai shekaru 200 da rubutawa a lardin Asyut da ke kasar Masar wanda shi ne mafi karanta akasar.
Tun a zamanin khalifancin dalar Usmaniyyah a ka rubuta wannan kur’ani wanda tsawonsa ya kai CM 2 baki daya.
Ahmad Kasim shi ne shugaban bangare bincike kn abubuwan tarihi a ami’ar Asyut ya bayyana cewa, sun jima da gano wanan kur’ani, amma ba si sanar bam sabioda suna gudanar da bincike ne akansa, amma bayan kammala binciekn sun yi baynai a kansa.
Ya ce bisa ga abin da bincikensu ya tabbatar musu, wannan kur’ani ya kai kimanin shekaru 200 da rubuta shi, wato tun farkon hukuncin daular Usmaniyya a kasar.
Ya kara da cewa kur’anin an lullube shi da fata wadda aka yi ado da zinariya, kuma kuna a nyi rubutun larabaci da kuma trkancin a kan bangonsa.
Wasu daga cikin mutanen kasar Masar suna zuwa wannan wuri domin ganewa idanunsu wannan kwafin kur’ani mai tsarki da ake byyan shi da cewa shi ne yafi karanta akasar baki daya, wanda tsawonsa ya kai CM 2 kawai, fadinsa kuma Ml 25 kamar yadda aka bayyana.
Yanz haka dai wannan kwafin kur’ani ya shiga cikin kayan tarihi na kasar wadanda ake adanawa, wanda suke kima babba, kuma za a ci gaba da ajiye shi a dakin kayan tarihi na bangaren bincike na wannan jami’a.




