IQNA

Gyara Tunanin Mutane Maras Kan Musunci A Amurka

22:26 - April 18, 2016
Lambar Labari: 3480333
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zaman taro na mata musulmi da nufin gyara tunanin masu adawa da muslunci a kasar saboda rashin sani.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Wrex cewa, a wurin taron Lissa Zainab Kilinger wata wadda ta karbi addinin muslunci a kwanakin baya.

Ta yi Magana kan muhumman lamurra da da ya kamata sauran mustane wadanda ba musulmi da ya kamata su sani dangane da addinin msulunci a kasar.

Daga ciki kuwa har da yadda suke daukar cewa shi addinin muslunci addini ne na ta’addanci, alhali kuwa shi addini ne na zaman lafiya da fahimtar juna da kuma tausayin bil adama da jin kansa a kowane lokaci.

Lamis Diyab wadda ita ma daya daga cikin mambobin wannan cibiya da ta shirya gudanar da zaman taron, ita ma ta gabatar da nata jawabinta ga mahalarta taron, ida ta yiishara da abin da ya kamata a fahimta dangane da addinin muslunci da kuma tsarinsa.

Ta bayyana cewa saboda abin da yak e faruw a duniya na ta’addnci, wannan ya sanya wadandsa ske da matsalar yamar msuumi suna yin amfani da wannan damar wajen kara bakanta sunan muslunci a duniya, alhli kuwa abin da yake faruwa bas hi da wata alaka da addinin muslunci.

3489728

captcha