IQNA

An Fara Gudanar Da Gasar Karatun Kur’ani Ta Kasar Somalia

20:25 - April 19, 2016
Lambar Labari: 3480335
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da bababr gasar kur’ani ta kasa baki daya a birnin magadishou na kasar Somalia.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na alshahid.net cewa, adaga jiya ne aka fara gudanar da bababr gasar kur’ani ta kasa baki daya a birnin magadishou na kasar Somalia wadda ita gasa mafi girma wadda ta hada harda da kuma karatu, wanda zai ci gaba har kwanaki 5 a nan gaba.

Bisa la’akari da cewa wannan gasa it ace mafi muhimamnci a kasar, dukkanin wakilai daga jahohi 18 na kasar suna halartar gasar.

Yusf Hussain Jum’ali, magajin garin magadishou, Umar Faruk Sheikh Abdulaziz mataimakin ministan ma’aikatar kula da harkokin addini su ne manyan baki a wannan taron bude gasa, kamar yadda kuma aka samu halartar malamai da kuma wasu jami’ai na kasar.

Muhamamd Abdulganiy sizu shi ne shugaban cibiyar da ke daukar nauyin shirya tarukan karatun kur’ani da kuma gasa, ya kuma gabatar da jawabin bude taro, tare da yin Karin haske kan taron da kma abbuwan da za a gudanar.

3490056

captcha